Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Na Gina Makarantu Bayan Hare-Haren Boko Haram


Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya

A kokarin da ta ke yi ta ga cewa ba a bar 'yan makarantar firaimare a baya ba, gwamnatin Kamaru ta kaddamar da wani shirin gina makarantu bayan da 'yan kungiyar Boko Haram su ka rusa wasu da dama.

Gwamnatin Kamaru ta kaddamar da wani shiri na gaggawa inda za ta kashe Dala miliyan takwas wajen gina ajujuwan karatu akalla guda 200.

Shirin har ila yau zai ba da damar gina ban-daki dubu 70 da kuma dakunan kwanan dalibai wadanda ‘yan kungiyar Boko Haram su ka lalata a hare-haren da su ka kai.

A cewar hukumomin Kamaru za a gina makarantun ne a yankunan da ba sa fuskantar barzanar masu ta da kayar bayan.

Gwamnan yankin arewa mai nisa da ke Kamarun, Midjiyawa Bakari, ya ce akalla makarantu 170 ‘yan kungiyar Boko Haram su ka barnata, ya kuma kara da cewa yanzu haka an ba da kwantirigin gina makaratun ga ‘yan kwangila da ba za kawo tsaiko ba inda ake sa ran za su kamala gina makarantun cikin kwanaki 40.

Daya daga cikin masu hidimar gina makarantun ya ce gwamnati ta share musu fagen fara gine-gine ta hanayr kawar da duk wani kalubale da ka iya kawo cikas wajen kammala gina-ginen.

Baya ga haka rahotanni na cewa an tura jami’an tsaro zuwa wasu daga cikin yankunan da za a yi aikin domin a baiwa ma’aikata kariya.

Kiyasin da aka na nuni da cewa mafi yawan daliban da aka lalata musu makarantu, dalibai ne na Firaimari wadanda yawansu ya kai dubu 33 wadandan kuma makarantunsu ke kusa da kan iyakar Najeriya.

Wadannan dalibai na daga cikin mutane dubu 150 da ‘yan kungiyar Boko Haram su ka tilastawa ficewa daga muhallansu tun bayan da su ka kaddamar da hare-harensu a yankunan.

Kasancewar ta hada kan iyaka da kasar Najeriya, Kamaru ma ta yi fama da hare-haren 'yankungiyar Boko Haram a 'yan kwanakin nan.

XS
SM
MD
LG