Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Bari Garuruwa Su Koma Hanun Boko Haram Ba- Omeri


Wasu 'yan gudun hijra da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu
Wasu 'yan gudun hijra da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu

Bayan kwato wasu garuruwa da dakarun hadin gwiwa hade da na Najeriya su ka yi, gwamnatin kasar ta ce ta dauki matakan kare aukuwar hakan.

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta bari garuruwan da aka kwato daga hanun Boko Haram su sake kubucewa ba.

A wata hira da Jami’in da ke kula da hukumar samar da bayanai kan ayyukan ta’addanci, Mr. Mike Omeri, ya ce dakarun Najeriya na ci gaba da samar da tsaro a wadannan wurare.

“Musamman domin ka da a koma gidan jiya, sojoji da ‘yan sanda su nan suna karfafa ayyukansu na tsaro a wadannan wurare.” In ji Omeri.

Ya kuma kara da cewa akwai bukatar mazauna wadannan garuruwa su dinga samar da bayanai da su ke ganin za su iya kawo cikas ga zaman lafiya a wadannan wurare.

Baya ga mazauna wadannan garuruwa, Mr Omeri ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su dinga lura da abubuwan da ke faruwa a tsakaninsu.

A ‘yan kwanakin nan dakarun hadin gwiwa da su ka hada har da na Najeriya sun kwato wasu garuruwa a yakin da su ke fama da rikicin Boko Haram.

Ba Za Mu Bari Garuruwa Su Koma Hannun Boko Haram Ba - 4'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG