Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa ‘yan kungiyar Boko Haram suna kara sake tattaruwa a garin Gwoza inda suka fi karfi, yayinda kuma suke neman tallafin mayaka daga wadansu wurare.
Wani dan leken asiri dake sa ido kan yadda lamaran ke gudana ya shaidawa Muryar Amurka cewa, rundunar soji tana kara dosar garin, yana yiwuwa kuma mayakan na shirin jan daga ne a Gwoza, daya daga cikin manyan gagaruwuwan dake karkashin ikon kungiyar a arewa maso gabashin Najeriya.
Majiyar tace mayakan dake kan hanyarsu zuwa marawa Boko Haram baya, suna fitowa ne daga jejin Sambisa inda suke buya.
Garin Gwoza na tazarar kilomita dari da talatin da biyar da Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya laburta cewa, mayakan sun yiwa garin kawanya da nakiyoyi da suka binne a karkashin kasa yayinda suke gargadin jama’a su fice daga garin.Rahoton ya nuna cewa, kungiyar ta saki wadansu mata majiya karfi da take tsare da su.
Majiyar Muryar Amurka tace a cikin makon nan mayakan suka kashe wadansu fararen kaya a Gwoza da suka ki daukar makamai su taya su jan daga a garin.