Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaman Sasanta Rikicin Sudan ta Kudu ya Sake Samun Cikas


Shugaban sabuwar kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir.
Shugaban sabuwar kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir.

Kokarin nemo bakin zaren rikicin kasar Sudan ta Kudu ya sake samun cikasa bayan da aka kammala taro a yau juma'a ba tare da an samu matsaya guda ba.

A yau Juma’a an tashi bara-baran a zaman sasantawar da a ke yi tsakanin Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar a birnin Addis Ababa da ke kasar Ethiopia.

Mr. Machar dai ya dora laifin watsewar wannan tattaunawa akan gwamnati inda ya ce a bangarensu sun yi iya bakin kokarinsu na ganin cewa an samu mafita kan rikicin.

Amma a cewarsa matsayar da gwamnati ta dauka na kawo cikas ga tattaunawar domin ba za su amince da cewa an ci nasara a kansu ba.

Koda ya ke Machar ya ce za su jira su ga matakin da Firaiministan Ethiopia Hailemariam Deslegn zai dauka kan yadda za a ci gaba da neman bakin zaren rikicin.

Rahotanni sun ce Mr. Desalegn ya ce ba za su amince da ci gaba da tsawaita wannan yaki ba domin abin da ke faruwa a Sudan ta kudun ya sabawa tunani da ka’idojin siyasa.

Sai dai a daya bangaren Ministan yada labaran Sudan ta Kudu, Michael Makuei, ya ce ana bukatar lokaci kafin a samu matsaya guda wadda za ta farantawa kowa da kowa, wato kan yadda za a kafa gwamnatin hadin gwiwa.

Ya kuma kara da cewa kuskure ne a ce tattaunawar ta ruguje baki daya domin a ganin shi an samu ci gaba a zaman da a ke yi.

A baya Majalisar Dinkin Duniya ta sa ranar 5 ga watan Maris din nan a matsayin wa’adin da za ta fara kakaba takunkumi hana tafiye-tafiye ga duk wanda a ke ganin su na kawo cikas a kokarin da a ke yi na shawo kan rikicin.

A dai shekarar 2011 ne kasar ta Sudan ta Kudu ta samu ‘yancin gashin kanta daga Sudan, inda daga baya kasar ta tsunduma cikin rikicin siyasa tsakanin Shugaba Kiir da mataimakinsa Machar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane yayin da akalla mutane miliyan biyu su ka fice daga muhallansu.

XS
SM
MD
LG