An sako baturiyar nan ‘yar shekaru 71 dake aiki mishan da aka sace watan jiya a tsakiyar Najeriya.
Majami’ar Methodist dake nan Amurka tace an mika Phyllis Sortor ga shugabannin darikar.
Bishop David Kendall ya bayyana a wata sanarwa da aka buga a shafin yanar gizo na majami’ar cewa, Sortor ta san aikinta yana da hatsari, sai dai ta kuma sani cewa wurare kalilan ne a duniya da basu da hatsari.”
Sortor da aka sace a harabar makarantar Hope Academy dake Emiwroro jihar Kogi, ta taka rawa gaya wajen kafa makarantu da dama a jihar Kogi domin ilimantar da ‘ya’yan Fulani makiyaya.
Tashar NBC News ta bada rahoto cewa, wadanda suka yi garkuwa da Sortor sun tuntubi aminiyarta suka nemi a biyasu diyyar dala dubu dari uku.
Kungiyar Boko Haram bata kai hare hare a jihar da aka sace ma’aikaciyar mishan din.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kogi ya fada a lokacin da aka sace ta cewa, ya hakikanta, garkuwa da ita da aka yi aikin masu aikata miyagun laifuka ne.