‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 3 A Katsina

Yan bindiga

An harbi wani likita da ke bakin aiki a daren Talatar da ta gabata, sa’ilin da gungun ‘yan bindiga ya mamaye babban asibitin Kankara a jihar Katsina da ke shiyar arewa maso yammacin Najeriya.

Gungun ‘yan bindigar ya harbi likitan, Murtala Saleh, a cinyarsa ta dama, sannan ya raunata wani mutum, Kamala Suleiman, a gwiwa.

‘Yan sanda sun ce dukkanin mutanen 2 na samun kulawar likitoci kuma suna cikin hayyacinsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Abubakar Aliyu yace jami’ansu sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar da ke rike da bindigogi kirar ak-47, amma batagarin sun yi nasarar yin garkuwa da mutane 3 yayin gumurzun.

“Ana kokarin ganin an kubutar da mutanen da aka sace cikin amince tare da kamo wadanda suka aikata mummunan aikin,” kamar yadda ya bayyana a cikin sanarwar daya fitar a jiya Laraba.