Wasu mazaje masu aikin ba da kariya ga yankunan su daga harin ‘yan bindiga sun gamu da ajalinsu a lokacin da suke kokarin kai dauki a kauyen Tungar Kara na gundumar Boko a Karamar hukumar Zurmi da kuma Kauyen Dangebe a gundumar Gidan goga a Karamar hukumar Maradun wadanda ke makwabta da juna a jihar Zamfara.
Shugaban masu aikin tsaron yankin, Amadu Baushi Malikawar Kube, ya ce jirgin sama ne ya sako masu wani abu da suke kyautata zaton bom ne har ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen da kuma raunata wasu.
Ya ce “Akalla an kashe mana mutum 30 wasu 15 kuma sun samu raunuka. Jirgin sama ne na sojoji ya sako mana bom lokacin muna dauke da dogayen bindigogi na gargajiya kuma mun daga hannuwan sama, amma a haka ya sako man bom.”
Wani daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya, Ya’u Malikawa ya ce suna kan hanya ne zuwa kai dauki ne a kauyen Dangebe da Tungar Kara inda ‘yan bindiga suka kai hari, sai suka samun labarin cewa ‘yan bindigar sun fita shine suka juye sai jirgin yayo kan su.
Masu aikin tsaron da ake kira ‘yan sa-kai sun fito daga Kauyukan Malikawa, Tungar Keta, Hemawa, Tungar Labbo, Gidan Goga da Gyaddo, wadanda suka hadu don kai dauki su yaki Kauyukan, a cewar daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.
A nashi bangaren, Dan majalisar da ke wakiltar yankin a Majalisar dokokin Jihar Zamfara, Hon. Maharazu Salisu Gado Faru, wanda ya bada tabbacin faruwar lamarin ya ce jirgin sama ne na soji yaje kai dauki akan harin ‘yan bindiga a yankin, sai ya sako bom a kan mutanen.
Ya ce jirgin saman sojin Najeriya a bisa kuskure ya jefa bom a kan masu aikin ba da tsaro ga yankunan su. Muna nan muna daukar matakan ganin an kula da mutanen da lamarin ya shafa.
Ya kara da cewa, har yanzu dai ba a kai ga tantance ainihin adadin mutanen da suka mutu ba a sakamakon lamarin.
Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren ‘yan bindiga ke kara kamari a jihar ta Zamfara.
Saurari cikakken rahoton Abdulrazaq Bello Kaura:
Dandalin Mu Tattauna