Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin 'Yan Bindiga Ya Hallaka Mutane 7 A Nasarawa


Yan bindiga
Yan bindiga

Kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa , Shettima Muhammad,  ya jagoranci tawagar jami'ansa zuwa wurin inda suka gano gawawwaki 7 tare da bin sawun maharan.

Al'ummar kauyen Tatara na karamar hukumar karu ta jihar nassarawa sun fada cikin firgici sakamakon harin 'yan bindigar da ya hallaka mutane 7.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Sp Ragman Nansel, ne ya bayyanawa tashar talabijin ta channels cewar harin ya afku a daren Asabar din da ta gabata.

Ya kara da cewar 'yan sanda sun samu kiran gaggawa kuma nan take, kwamishinan 'yan sandan jihar, Shettima Muhammad, ya jagoranci tawagar jami'ansa zuwa wurin inda suka gano gawawwaki 7 tare da bin sawun maharan abinda ya tilasta musu yin watsi da baburansu 9.

Ya ci gaba da cewa nan take kwamishinan 'yan sandan ya kira taron masu ruwa da tsaki inda ya yiwa iyalan wadanda suka mutu ta'aziya tare da bada umarnin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

An tura jami'an 'yan sanda zuwa yankin domin tabbatar da tsaro sannan an tsara cewar gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Sule zai ziyarci wurin.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG