Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Hallaka Sojojin Najeriya Bayan Kammala Jana’izar Mutanen Da Hari Ya Rutsa Da Su


Fadan ya barke ne a ranar Talata lokacin da sojojin ke dawowa daga birne manoman da aka kashe kwanaki 2 da suka gabata a kauyen Dumba da ke gabar tafkin Chadi

Fafatawa tsakanin hukumomin tsaron Najeriya da mayakan boko haram ta hallaka sojoji 9 a arewa maso gabashin kasar, wasu dakarun soja 2 ne suka shaidawa afp hakan a yau Alhamis, kwanaki bayan da wata kungiyar ‘yan jihadin dake adawa da ita ta harbe gamman manoma.

Fadan ya barke ne a ranar Talata lokacin da sojojin ke dawowa daga birne manoman da aka kashe kwanaki 2 da suka gabata a kauyen Dumba da ke gabar tafkin Chadi, a cewar dakarun.

“Mun rasa 9 daga cikin sojojinmu a musayar wuta da ‘yan ta’addar Boko Haram sannan wasu 5 sun bata,” a cewar daya daga cikin dakarun.

An kuma jikkata soja guda, ya kara da cewa.

“Sojoji 7 sun mutu nan take yayin da 2 daga cikin wadanda suka jikkata suka cika a asibiti daga bisani,” kamar yadda soja na 2 ya shaidawa afp.

Sojojin na dawowa ne daga kauyen Tumbun Kanta inda suka taimakawa mazauna garin birne manoman da mayakan iswap suka hallaka a Lahadin data gabata a matsayin hukuncin yin kutse cikin yankinsu bada izini ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG