Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Koma Jihar Neja Bayan Sulhun Kaduna


Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago

'Yan bindigar Kaduna sun koma jihar Neja da aika aikarsu


A yanzu haka dai al,ummomin da ke zaune a kananan hukumomin Shiroro da Muya da kuma Rafi a jihar Nejan Nigeria masu iyaka da yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun ce tun bayan yin sulhu tsakanin gwamnatin Kaduna da 'yan bindigar yankin na Birnin Gwarin su ka shiga cikin yanayi na tashin hankali,

Wadanda muka zanta da su daga wadan nan kananan hukumomi sun ce a yanzu wadan nan 'yan bindiga suna shigowa jihar Neja ne su tabka ta'asarsu, lamarin da ya sa suke zaune cikin yanayi na zaman zullumi,

Amma Gwamnan Jihar Nejan Umar Muhammed Bago ya ce shi ma yana shirye da bin sahun jihar Kadunan na yin sulhu da 'yan bindigar,

Alhaji Usman daga Karamar Hukumar Shiroro ya ce tun bayan yin sulhun na Birnin Gwarin lamarin yin garkuwa da mutane domin Neman kudin fansa ya kara ta'azzara a yankinsu domin kuwa ko da yammacin jiyama sun kutsa wani kauye mai suna Afaka suka kwashe kimanin Mutane 20.

Shi ma Malam Muhammadu daga karamar hukumar Rafi yayi karin haske akan yadda wadan nan 'yan bindiga daga jihar Kaduna ke shigowa yankunansu Lamarin da ya ce yana matukar tayar da hankalinsu.

Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce tana Daukar Mataki domin dakile masu kutsowa jihar domin yin ta'addanci a cikin zantawa da shi Gwamna Umar Muhammed Bago ya ce kofarsu ta na bude domin yin sulhu da wadannan 'yan bindiga ta yadda za a samu zaman lafiya.

Da ma yankin na shiroro ya na fama da yawan kai hare hare har ma da fashewar bama bamai a baya da hukomi a jihar Nejan su ka ce mayaka ne na kungiyar Boko Haram da su ka yi sansani a dajin ke aikatawa.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG