Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Sojin Saman Najeriya Sun Musa Kashe Fararen Hula a Jifar Zamfara


An Tura Jirgin Yaki Mai Saukar Ungulu Zamfara
An Tura Jirgin Yaki Mai Saukar Ungulu Zamfara

“Dakarun sojin saman Najeriya suna takatsantsan wajen tabbatar da ragewa barna da kiyaye abka ma fararen hula a ayyukan da suke aiwatar wa.

Hukumar dakarun sojin saman Najeriya ta musa rahoton kashe fararen hula 16 a wani harin saman da jami’an ta suka auna ‘yan bindiga a yankin Tungar Kara a karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Wani labarin da mujallar Zagazola Makama, mai wallafa labaran ta’addanci a yankin tabkin Chadi, ta wallafa a ranar Lahadi, ta ruwaito cewa wata majiyar leken asiri ta ce wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da ‘yan kungiyar sa kai na Zamfara Community Protection Guard (ZCPG), da mazauna al’ummar.

Sai dai a hirar shi da kafar labaran yanar gizo The Cable, darektan sashen hulhda da jamma’a na rundunar sojin saman Najeriya, Olusola Akinboyewa, ya musa zargin.

Akinboyewa y aceDakarun tsaron saman Najeriya suna takatsantsan wajen tabbatar da ragewa da kiyaye farma fararen hula a ayyukan da suke aiwatar wa.

“Akwai yiwuwar cewa ‘yan ta’addan da magoya bayan su ne suke yada rahoton a yunkurin karyata sojoji da farfaganda, duba da cewa suna shan kashi.”

Akinboyewa y ace babu sahihan rahotanni akan fararen hular da harin ya rutsa da su kuma an kai harin saman bisa sahihan bayanan sirri ne. Akinboyewa ya kara da cewa, “Duk da haka, ku tabata cewa dakarun sojin saman Najeriya tana dogaro da kwararan sahihan bayyanan sirri ne a yaki da ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da take yi daga majiyoyi mabanbanta sannan kuma a sake yin bincike don tabbatar da bayanan.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG