Wasu gungun ‘yan bangar siyasa ne suka kai hari akan wasu kusoshin jam’iyar APC dake adawa da tazarcen gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindow Jibrilla, batun da yanzu haka ma ke bude wani sabon shafi a fagen siyasar jihar dake cike da rikici.
An dade ana ta kai ruwa rana a tsakanin ‘yan bangaren tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako, da Nuhu Ribadu da kuma bangaren tsohon sakataren gwamnatin tarayya Mista Babachur David Lawal, da kuma ‘yan bangaren gwamnan jihar Bindow Jibrilla a bangare guda.
Alhaji Ibrahim Usman Jimeta, na cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya yayin harin da aka kai, kuma ya bayyanawa Muryar Amurka yadda lamarin ya faru.
Ya ce suna zaune ne suka fara jin ihun wasu mutane na cewa ‘Sai Bindo, karya ake yi sai Bindo, sai Sulaiman’ kuma lekawar da suka yi domin ganin abin da ke faruwa, sai suka ga an farfasa musu motoci. Nan take suka bugawa mataimakin kwamishinan ‘yan sanda waya, wanda kuma ya tura jami’an ‘yan sanda zuwa wajen.
To sai dai tuni gwamnan jihar ta bakin kwamishinan yada labaran jihar Ahmad Sajo, ya musanta zargin cewa su ne suka sa, aka kai wannan harin, inda gwamnan ya ce ai wasu ne kawai ke son bata masa suna.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar harin, kuma ta babbatar da cewa tana bincike akai.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5