‘Yan Adawa A Nijar Sun Bukaci A Binciki Tsohon Shugaba Issouhou Mahamadou

Shugaba Issouhou Mahamadou

A Jamhuriyar Nijar, wani ce-ce-ku-ce ya barke a tsakanin bangarorin kasar bayan da ‘yan adawa suka zargi tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou da siyen wani fili mallakar gwamnati alhali doka ba ta yarda da haka ba. Sai dai makusantansa na kallon abin tamkar rashin sanin abin fada  ne.

Ainihi wani jigo a babbar jam’iyar adawa ta Moden Lumana Bana Ibrahim ne ya fara bankado wannan labari a shafinsa na Facebook bayan nazarin bayanan da rahoton kotun Cour des Comptes na 2020 ya kumsa game da dukiyoyin da Issouhou Mahamdou ya mallaka kafin ya sauka daga kujerar shugabancin kasa.

Bana Ibrahim na ganin ya zama wajibi kotun ta Cour Des Comptes ta sake waiwayar tsohon shugaban kasar ta Nijar domin ya yi wa jama’a cikakken bayani kamar yadda doka ta tanada.

Sai dai makusantan tsohon shugaban kasar na cewa babu kamshin gaskiya a wannan zargi da suke dauka a matsayin wani batu ne mara tushe.

Kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar ne ya umurci kowane daga cikin shugabanin kolin kasar, ya yi wa kotun Cour Des Comptes bayani game da adadin dukiyar da ya mallaka kafin soma aiki.

Sannan wajibi ne ya sanar da jama’ar kasa abin da ake ciki game da wadannan kadarori a kowace shekara dalili - kenan ‘yan adawa ke ganin bukatar sake duba bayanan da tsohon shugaban kasa ya gabatarwa kotun watanni kadan kafin ya sauka daga karagar mulki.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Adawa A Nijar Sun Bukaci A Binciki Tsohon Shugaba Issouhou Mahamadou