La’akari da yawaitar tashe-tashen hankula masu nasaba da ayyukan ‘yan bindiga da na ‘yan ta’addan da suka addabi al’umar Nijar da ma kasashe makwabta, ya sa kungiyar hada kan kabilun Nijar Les Nigeriens Sont Des Cousins, shirya taron domin addu’oin zaman lafiya
A daidai lokacin wadanan addu’oin kungiyar NSC ta rarrabawa wasu kananan yara marayu kayan sallah domin ba su damar samun walwala a yayin bukukuwan karamar sallar da ke tafe.
Sakataren kungiyar malaman makaranta ta SNEN Issouhou Arzika da ke daya daga cikin manyan baki ya jinjinawa wannan yunkuri da ya ce abu ne da ke bukatar samun goyon bayan al’umma.
Wannan dai shi ne karo na biyu da kungiyar hada kan kabilu NSC, ke shirya taron addu’o’in zaman lafiya albarkacin watan Ramadan, tare da baiwa yara marayu tallafn kayan sallah.
Wannan tsari a cewar shugabanninta, ya sa suka kuduri aniyar ci gaba da shiryawa lokaci zuwa lokaci a matsayinta na kungiyar da ba ruwanta da manufofin siyasa.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.