Da safiyar ranar Labara ne shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazum tare da mambobin gwamnatin Farai Minista Uhumudu Mahamadu da shugaban Majalisar Dokokin kasar, Seyni Omar, da kuma sauran shugabannin al’umma suka halarci sallar Idi a masallacin El-Kaddafi da ke birnin Yamai.
Duk da yake an gargadi Musulmai da su guji daukar kananan yara zuwa sallar Idi, amma duk da haka an fito sosai inda yaran suka runtuma fadar shugaban kasa don yi masa barka da sallah, tare da kiyaye matakan kare kai daga kamuwa da cutar coronavirus.
Shugabanni sun yi kira ga al’umomi da su ci gaba a yin addu’o’in neman sauki ga matsalar rashin tsaro da ta addabi kowa, tare da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Kasancewar wasu kalilan ne suke bikin karamar sallah a makwabciyar kasar Najeriya, rahotanni na nuni da cewa mazauna yankunan iyakar kasar Nijar, sun tsallaka Jamhuriyar domin haduwa da sauran Musulmi ‘yan uwa wajen gudanar da bukukuwan karamar sallah.
Da yawa daga cikin manyan kasashen Musulmi a duniya sai gobe Alhamis ake sa ran za su yi karamar sallah, ciki har da Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Mamman Bako.