Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahamat Idriss Deby Ya Kai Wa Bazoum Ziyara A Nijar


Shugaban rikon kwarya a Chadi, Mahamat Idriss Deby, hagu da Shugaban Nijar Bazoum Mohamed, dama (Hoto: Fadar shugaban Nijar)
Shugaban rikon kwarya a Chadi, Mahamat Idriss Deby, hagu da Shugaban Nijar Bazoum Mohamed, dama (Hoto: Fadar shugaban Nijar)

Kwana 1 bayan da rundunar mayakan Chadi ta bada sanarwar murkushe dukkan wani kutsen ‘yan tawayen FACT, Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar General Mahamat Idriss Deby, ya kai ziyara a Jamhuriiyar Nijar a ranar Litinin 10 ga watan Mayu inda suka tattauna da shugaban kasa Mohamed Bazoum a fadarsa.

Muhimman batutuwa 2 ne aka tattauna akansu a yayin wannan ziyara ta shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Chadi General Mahamat Idriss Deby.

Na farko ya yi wa shugaba Mohamed Bazoum bayani a dangane da halin da ake ciki game da tafiyar gwamnatin rikon kwaryarda aka kafa bayan rasuwar shugaban kasar Chadi Marechal Idriss Deby.

Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby Ya Kai Ziyara Nijar
Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby Ya Kai Ziyara Nijar

Deby ya ce ya kai ziyarar ce don kara jaddada girman dangantakar dake tsakanin Chadi da Nijar sannan kuma ya yi wa dan uwansa Mohamed Bazoum godiya saboda gudunmawar da yake ba Chadi bayan rasuwar Marshal Idriss Deby.

Karin bayani akan: Mahamat Deby, Mohamed Bazoum, Idriss Deby, FACT, Jamhuriyar Nijar, kasar ta Chadi, da Chad.

Masu rajin kare dimokradiya irinsu kungiyar MOJEN Siraji Issa na kallon wannan ziyara a matsayin wata alamar haske game da nauyin da aka dorawa shugaban Nijar Mohamed Bazoum mai alhakin sasanta bangarorin kasar Chadi.

Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby Ya Kai Ziyara Nijar
Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby Ya Kai Ziyara Nijar

Batu na biyu shi ne, wanda ya shafi harakar tsaro kasancewar kasar Chadi na taka rawa sosai a yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi da yankin Sahel.

A nan Mahamat Deby ya ce kamar yadda aka sani suna da dakaru dake da sansani a garin Tera wadanda ke aikin tsaro a karkashin rundunar G5 Sahel saboda haka zai je ya jajanta masu rasuwar Marshal Idriss Deby sannan kuma ya kara masu kwarin gwiwa domin su ci gaba da aiki ba gajiya.

Mai sharhi akan sha’anin tsaro Abdourahamane Alkassoum na ganin ziyarar ta General Mahamat Idriss Debyza ta yi tasiri sosai a kawunan dakarunsa dake fagen daga.

Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby Ya Kai Ziyara Nijar
Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby Ya Kai Ziyara Nijar

Kasar Chadi mai fama da tarzomar wasu daga cikin ‘yan adawa da kungiyoyin fararen hula masu kin jinin gwamnatin da ta gaji marigayi Idriss Deby ta bada sanarwar murkushe kungiyar ‘yan tawayen FACT a karshen makon jiya bayan shafe kusan wata 1 ana gwabza fada a kokarinsu na shiga birnin N’djamena.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Mahamat Idriss Deby Ya Kai wa Bazoum Ziyara A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG