Yaki Da Hamas Bai Kare Ba Ko Bayan Tsagaita Bude Wuta - Netanyahu

Shugaban Isra’ila Benjamin Netanyahu

A ranar Talata Isra'ila da Hamas sun kusa cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta na wani dan lokaci a yakin da suke yi na tsawon makwanni shida a dalilin dimbin Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza da nufin yin musanya da Falasdinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.

WASHINGTON, D. C. - To sai dai yayin da Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kira taron majalisar ministocinsa domin kada kuri'a, ya sha alwashin ci gaba da kai farmakin da Isra'ila ke kaiwa kan Hamas da zarar an kawo karshen wa'adin tsagaita wutar.

"Muna cikin yaki, kuma za mu ci gaba da yakin," in ji shi. "Za mu ci gaba har sai mun cimma dukkan burinmu."

Ana sa ran majalisar zartaswar Isra'ila za ta kada kuri'a kan wani shiri da zai dakatar da hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza na tsawon kwanaki domin musanyar kusan mutane 50 daga cikin 240 da Hamas ta yi garkuwa da su.

Isra'ila ta sha alwashin ci gaba da yakin har sai ta karya karfin soji na Hamas tare da mayar da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su. Taron majalisar ministocin ya ci gaba da gudana har zuwa safiyar Laraba.

-AP