Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zanga-zangar Goyon Bayan Falasdinawa A London, Za A Yi Ta Goyon Bayan Isra’ila A Paris


Yadda aka baza 'yan sanda a birnin London a lokacin zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa
Yadda aka baza 'yan sanda a birnin London a lokacin zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa

Sama da jami’an tsaro dubu uku za a baza a birnin na Paris don su tabbatar da tsaro yayin tattakin a cewar Ministan cikin gida Gerald Darmanin.

Sama da masu zanga zangar nuna goyon bayan Falasdinawa dubu 300 ne suka yi tattaki a tsakiyar birnin London a ranar Asabar, a gefe guda kuma ‘yan sanda suka kama masu tsattsauran ra’ayin mazan jiya kusan 100 da suka fita da niyyar nuna adawa da zanga-zangar.

‘Yar hatsaniya ta kaure a tsakanin ‘yan sanda da masu tsattsauran ra’ayin wadanda suka taru don su nuna adawwarsu da tattakin wanda ya fado daidai da ranar tunawa da lokacin da aka kawo karshen yaki duniya na daya da tunawa da ‘yan Birtaniya da sauran ‘yan wasu kasashe da suka mutu a yakin.

Firaiminista Rishi Sunak ya yi Allah wadai da tarzomar da ta barke tare da sukar masu nuna “goyon bayan Hamas” wadanda suka yi dandazo suna ta rera wakokin nuna kyamar Yahudawa dauke da alluna da riguna da aka rubuta sakonnin goyon bayan Falasdinawa.

Tun kafin tattakin na ranar Asabar ake ta ta da jijiyar wuya, tattakin da ya zamanto mafi girma cikin wadanda ake yi don nuna goyon bayan Falasdinawa tare da yin kiraye-kirayen a dakatar da bude wuta a yankin Zirin Gaza bayan da ministan cikin gida Suella Braveman ta kira gangamin a matsayin “na nuna kiyayya” da tsageru ke jagoranta.

A gefe guda kuma a yau Lahadi ake sa ran za a yi wani tattakin yin Allah wadai da nuna kyamar Yahudawa a Paris babban birnin Faransa yayin da ake ta ce-ce-ku-ce a tsakanin jami’yyun siyasa kan wa ya kamata ya halarci tattakin, a kuma daidai lokacin da ake ganin karuwar nuna kyama ga Yahudawa a sassan kasar ta Faransa.

Sama da jami’an tsaro dubu uku za a baza a birnin na Paris don su tabbatar da tsaro yayin tattakin a cewar Ministan cikin gida Gerald Darmanin.

A jajiberin ranar da za a yi tattakin, Shugaba Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da abin da ya kira “karuwar nuna kyama ga Yahudawa” a Faransa.

Cikin wata wasika da ya rubuta wacce aka wallafa a jaridar Le Parisien, Shugaba Macron ya ce kasar Faransar da Yahudawa za su rika fargaba a cikinta, ba Faransa ba ce, kazalika Faransar da mutane za su rika fargabar zama saboda addininsu ko asalinsu ba Faransa ba ce.”

Macron ya kara da cewa, tattakin da za a yi a yau Lahadi zai nuna Faransa a matsayin kasa mai madaurinta daya da take maraba da kowa da kowa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG