Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Fara Neman Hamas A Mabuyar Su Dake Karkashin Kasa


Israel Palestinians Controlling Gaza Explainer
Israel Palestinians Controlling Gaza Explainer

Yau Lahadi Isra’ila ta buga wani hoton bidiyo inda ta nuna wani rami da ta ce kungiyar ‘yan bindigan Falasdinu ce ta gina a karkashin asibitin Shifa dake zirin Gaza, yayin da ta maida hankali wurin nema da kuma lalata ayyukan kungiyar Hamas.

Duk da cewa ta amince tana da daruruwan hanyoyi na kilomitoci karkashin kasa, da ramuka da kwararo da hanyoyin bullewa a duk fadin yankin Falasdinu, Hamas ta musunta cewa wadannan hanyoyi nada alaka da gine gine fararen hula kamar asibiti.

A wani karin bayani a yau Lahadi a kan aikinta a Shifa, ma’aikatar sojin Isra’ila ta ce injiniyoyinta sun gano wani rami mai tsawon mitoci 10 kana yana shiga har zuwa mitoci 55 zuwa wata kofar da bam bai kamata.

“Kungiyar ta’addanci Hamas ta kan yi amfani da irin wannan kofa domin tare sojojin Isra’ila shiga inda suke da kuma hana su samun hanyar shiga inda kadarorin Hamas suke”, in ji wata sanarwar sojin Isra’ila wadda ta zo da hoton bidiyon dake nuna wani dan kwararo da aka yiwa rufin konkarai da ya kare a wata kofa mai ruwan toka.

An kashe akalla Falasdinawa biyu a cikin dare a wasu hare hare da Isra’ila ta kai a yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.

Akalla jarirai ‘yan bakwanni 31, kan kwashe su daga Asibitin Shifa kuma za a kai su wani asibiti a Masar, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya a yau Lahadi.

Wata tawagar hukumar lafiya ta duniya da ta kai ziyara a asibitin Shifa jiya Asabar, tace akwai jarirai 32 dake bukatar kulawa.

An kashe fararen hula da dasma wadanda suka rasa matsugunansu kana aka jikata wasu a jiya Asabar a wani farmaki ta sama da Isra’ila ta kai.

Ta kuma hari a wata a makaranta a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya dake arewacin Gaza, a cewar ma’aikatan jin kai na MDD da kungiyar taimakon ‘yan gudun hijira ta Falasdinawa.

Hotuna da kamfanin dillancin labarai na AP ya fitar ya nuna sama da gawarwaki 20 nade a cikin zani da jini ajiki.

A martaninta, ma’aikatar sojin Isra’ila tace sojojinta sun yi aiki a Jabaliya kadai ne, da zummar kaiwa ‘yan ta’adda hari, yayin da suke kokarin takaita cutar da farar hula.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG