Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila Na Shirye-shiryen Kutsawa Cikin Zirin Gaza


Wani lokaci a baya da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yake gaisawa da wani sojin saman Isra'ila
Wani lokaci a baya da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yake gaisawa da wani sojin saman Isra'ila

Kutsa kai da Isra'ilan take shirin yi cikin yankin na Gaza mataki ne na zakulo mayakan Hamas don mayar da martani ga mummunan harin da suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba

Rundunar sojin Isra’ila ta ce, dakarunta na fadada ayyukansu a yankin zirin Gaza, yayin da suke ci gaba da kusantar yankin don kaddamar da cikakkiyar mamaya a Zirin.

A ranar Juma’a hanyoyin intanet da na wayar salula suka katse a yankin na Gaza sanadiyyar zafafan hare-haren da Isra’ilan ke ta kai wa, lamarin da ya hana daukacin al’umar yankin da ya yawanta ya kai miliya 2.3 daga yin hulda da sauran al’umomin duniya da ma tuntubar junansu.

Isra’ila dai ta jibge dubban daruruwan dakarunta a kusa da iyakar yankin na Gaza.

Yadda hayaki ya tashi a Gaza bayan harin martani da Isra'ila ta kai yankin Gaza
Yadda hayaki ya tashi a Gaza bayan harin martani da Isra'ila ta kai yankin Gaza

Kutsa kai da Isra'ilan take shirin yi cikin yankin na Gaza mataki ne na zakulo mayakan Hamas don mayar da martani ga mummunan harin da suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba

A daren Juma’a an yi ta jin fashe-fashe a yankin wadanda suka rika haskaka sararin samaniyyar yankin na Gaza.

Babu dai tabbacin iya adadin mutanen da suka halaka a sabbin hare-haren na baya bayan nan saboda rashin hanyoyin sadarwa.

A halin da ake ciki, Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa tsarin ayyukan jin-kai a yankin na Zirin Gaza na fuskantar barazanar rugejewa baki daya, yana mai cewa idan ba a samu wadatattun kayayyakin jin-kai da man fetur ba, fararen hular da ke yankin za su fada mawuyacin halin da ba zai misaltu ba.

Antonio Guterres
Antonio Guterres

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Antonio Guterres ya ce dakika- bayan dakika, al’umar yankin na Gaza na kara fadawa cikin mummunan halin rayuwa.

Ya kara da cewa Majalisar Dinkin Duniya ba za ta iya ci gaba da kai kayayyakin agaji cikin Gaza ba idan har “ba a samu sauyi kan yadda al’amura ke gudana a yankin ba.”

Guterres ya kuma ce wajibi ne a sassauta ayyukan tantance kayayyakin da ake shiga da su ta Rafah domin a samu karin manyan motocin da za su kai kayayyaki cikin yankin wanda ke karkashin kulawar Hamas.

A gefe guda kuma, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce zai taimaka wajen samar da wata hadaka da za ta tallafa wajen samar da kayayyakin jin-kai don agazawa fararen hula Falasdinawa a yankin na Gaza.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Macron ya bayyana hakan ne bayan kwanaki biyu da shugabannin kungiyar tarrayar turai ta EU suka kwashe suna taro a Bruessels wanda aka kammala a ranar Juma’a.

A cewar Macron, za su kafa wata hadaka ta kasashen nahiyar turai da dama, ciki har da kasar Cyprus wacce za ta zama cibiyar ko kafa ta gudanar da ayyukan jin-kai.

A ranar Alhamis Macron ya ce za su tura jirage masu saukar ungulu zuwa yankin na Gaza don su tallafawa al’umar yankin.

Shugaban na Faransa, ya kuma jaddada kiran da yake yi wa Isra’ila da ta kare rayukan farar hula yayin da take kai hari kan mayakan na Hamas, tun bayan wani hari da suka kai a ranar bakwai ga watan Oktoba da ya halaka yahudawa 1,400 ciki har da sojoji da fararen hula.

The Hamas-controlled health ministry in Gaza has put the death toll at more than 7,000 Palestinians and more than 18,000 injured. Those numbers cannot be independently verified.

Ma'aikatar lafiya da Hamas ke kula da ita a yankin na Gaza, ta ce Falasdinawa sama da 7,000 aka kashe.

Sai dai babu wata kafa da ta iya tantance sahihancin wannan adadi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG