Wani matashin mawakin hip-hop Hamza Musa Yusuf, yace manufarsa da harkar waka shine jama’a su karbi wakokin da kuma yin amfani da abubuwan da wakokin suka kunsa ko kuma amincewa da sakon da wakokin suka kunsa inji Real DK mawakin Afro hip-hop amma fa na Hausa.
Yana mai cewa dalinlinsa na fara wake shine domin ware dank an matasa ‘yan uwansa kan harkokin duniya da su ka kunshi canje canjen da ake samu ta fuskar rayuwa.
Ya ce jigonsa a harkar ta waka na Afro a nan gida Nijeriya cikin har da mawaki Billy O, inda ya kara da cewa wakokinsa na nuni da kimanta sana’a tare da jan hankalin matasa da su jajirce wajen neman sana’a tare da nusar da su alfanun haka
Ya ce wakokinsa na jan hankali ‘yan arewa da su mike tsaye kada a barsu a baya , musamman ma a fanonin ciyar da kasar gaba
Real DK ya ce ya gamsu da wakokin da yake rerawa na fadakar da al’umma ganin yadda yake samun bayanan hakan a shafukan sada zumunta da masoya tare da shawarwari da suke badawa.
Your browser doesn’t support HTML5