Na gano cewa waka hanya ce ta aika sako cikin sauki ga dukkanin al'umma, tare da saukin isar da shi a lungu-lungu da sako-sako, a tabakin mawaki Nazifi Abdulasami Yusuf, wanda aka fi sani da Nazifi Asnanci.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA a Kano, inda yake cewa, a lokacin da ya shiga waka ya fuskanci gwagwarmaya, domin a lokacin da ya shiga sana’ar yayi karo da manyan mawaka wadanda samun shiga cikin su da al'umma sai an jajirce.
Ya kara da cewa dagewa da juriya ce ta kai shi ga matsayin da yake kai a yanzu, inda ya ke cewa a harkar nishadi ba dabi’a kasar Hausa ba ce, don haka harka ce da take cike da sammatsi da tsangwama ta hanyar samun masoya da kuma masu kushe sana’ar.
Ya ce rashin ganewa wadannan matsaloli ne ya haddasa wasu sabbin mawakan, barin sana’ar don rashin hakuri irin nasu. Amma hakuri da yayi da bin manya sauda kafa ya kai shi ga gacci, domin kuwa yana isar da sako kuma yana iya magance duk wasu matsalolin shi na rayuwa.
Facebook Forum