Ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tsaro NSA, Malam Nuhu Ribadu ya musunta zargin tura jami’ai zuwa masarautar Kano.
Wata babbar kotu da take Kano a Najeriya ta yankewa ‘dan China Frank Geng-Quangrong da ya kashe Ummulkhulsu Buhari har lahira a shekara 2022 hukuncin kisa ta hanyar rataya
A yau Talata ne shugaban kwamandan Hisbah ta jihar Kano Mal Aminu Ibrahim Daurawa ya koma bakin aikinsa biyo bayan murubus da yayi a makon da ya gabata bayan wani jawabi da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayi a gidan gwamnati yayin da yake ganawa da Malaman Addini.
Sheikh Aminu Daurawa ya dawo kan mukaminsa na Kwamandan Hukumar Hisbah, kwanaki kadan bayan yayi murabus.
Fitattaciyar ‘yar TikTok Murja Ibrahim Kunya ta shigar da kara gaban babbar kotun jihar Kano, bisa zargin keta mata haddi da rashin bin ka’idojin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar wajen shigar da karar da ake tuhumarta.
A safiyar yau Juma’a 1 ga watan Maris ne kwamandan Hisbah Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana ajiye aikinsa na shugaban hukumar a shafinsa na Facebook biyo bayan rashin samun goyon baya wajen gudanar da ayyukan kauda badala.
Kotun Shari'ar Musulunci da ke zamanta a Kano ta bukaci da a duba lafiyar kwakwalwar shahararriyar yar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya.
Bayan samun labarin ba wa Murjah Ibrahim Kunya beli, kafafen sadarwa ya cika da jita-jitar cewar Kwamandan Hisbah, Shiek Aminu Ibrahim Daurawa, ya ajiye aikinsa sakamakon ba da belin da kotu ta yi.
Biyo bayan kama fitattaciyar ‘yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya da rundunar Hisbah ta jihar Kano ta yi, tuni suka mikata ga kotu domin hukuntata.
A wannnan Shekarar da aka yi bankwana da ita ta ne wata matar aure, Hafsa Surajo, da a ke zargi da kashe abokin sana’arta ta hanyar caccaka masa wuka, alammarin da ya ja hankalin jama’a.
Wasu gungun matasa sun tada hargitsi a unguwar Kurna da ke karamar Hukumar Fagge a Kano da ya haddasa tada zaune tsaye. Lamarin da ya sa wani insifekta da ba a bashi umarni ba ya bude wa taron matasan da suke rikici wuta da yayi sanadin kashe wani matashi ya kuma raunata matasa biyu.
A ranar Talata ake sa ran za a yi jana'izar marigayin a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Nijar za ta fara fitar da gangan danyen mai dubu 90 domin siyarwa a kasuwannin duniya; Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta dauki tsauraran matakan tsaro na tabbatar da zabukan da aka gudanar ranar Asabar sun kammalu lami lafiya, da wasu rahotanni
Ra'ayoyin mutane akan karin Naira dubu 35 a wata ga ma’aikatan gwamnatin Najeriya, za su amfana? Ko wannan kari zai rage radadin cire tallafin man fetur? To wadanda ba za su amfana da wannan karin albashin kuma fa?
Yinkurin wasu masu niyyar daura auren jinsi ya ci tura bayan da hukumar Hisbah ta bankado shirin.
Kotun har ila yau, ta ba da umarnin kwace masallatansa guda biyu, tare da haramtawa kafofin yada Labarai na jihar Kano sanya wa'azinsa.
Domin Kari