Gwamnatin Amurka na binciken ko kamfanin Apple ya saba dokar kasuwar hannun jari kan manhajar da yake fitarwa don rage saurin tsoffin wayoyinsa idan batirinsu ya kusa mutuwa.
Ma’aikatar shari’a ta Amurka da hukumar dake kula da kasuwar, sun bukaci kamfanin Apple ya basu bayanai kan manhajar da ya fitar.
Binciken dai yana mayar da hankali ne kan ko Apple yana bin tsarin fitar da bayanai, kamar yadda ya amsa kukan da jama’a suka yi kan rage saurin wayoyinsu ‘yan makonni da suka gabata.
Ya bayyana ne a watan Disamba cewa Apple ya fitar da wata manhaja shekara daya da ta gabata da zata rage saurin tsoffin wayoyin iPhone lokaicn da batirinsu ya tsufa, da cewa wata dabara ce da zata kare wayoyin daga kashe kansu ba zato ba tsammani.
Apple dai ya musunta zargin da ake masa na cewa yana yin haka ne domin tilastawa masu amfani da wayoyin iPhone sayen sabbin wayoyinsa da ya fitar.
Facebook Forum