A jiya aka rufe hada hadar saye da sayarda ‘yan wasan kwallon Kafa na duniya a watan janairu, 2018.
Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon Kafa ta Arsenal, Mesul Ozil ya sabunta kwantiragin sa a kungiyar na tsawon shekaru biyu zuwa 2021 inda a baya kwantiragin zai kare ne a karshen kakar wasan bana.
Dan wasan Ozil, zai kasance dan wasan da yafi kowane dan wasa daukar albashi a kungiyar Arsenal, inda zai ke karbar kudi fam dubu £350, duk sati a matsayin albashi bayan an cire haraji.
Mesul Ozil, dan kasar Jamus, ya dawo Arsenal, ne a shekarar 2013 daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, bisa yarjejeniyar kwantirakin shekaru biyar a kan kudi fam miliyan £42.4 wanda a lokacin ya kasance dan wasan da yafi tsada a kungiyar.
A wasan Firimiya lig na bana, Ozil ya fafata a wasanni 21, kuma ya samu nasarar jefa kwallaye hudu, ya taimaka wajan jefa kwallaye shida.
Haka kuma yana cikin tawagar ‘yan wasan kasar jamus da suka lashe kofin kwallon Kafa na duniya a shekarar 2014. Ya kuma sami nasarar daukar kofin FA Cup har sau uku na kasar Ingila tare da Arsenal.
Facebook Forum