A na sa ran nan da ‘yan kwanaki shugaba Donald Trump zai sanar da cewa ba zai tabbatar Iran tana mutunta ka’idodin yarjejeniyar shirin makaman Nukiliyar da aka kula a shekarar 2015 ba, a saboda haka ya baiwa ‘yan majalissar dokokin Amurka kwanaki 60 su yanke shawara akan ko Amurka zata sanyawa Iran takunkumi ko a’a. Bisa doka, shugaba Trump na da har zuwa 15 ga watan nan na Oktoba don ya yanke shawara, amma wata majiya daga fadar White House ta ce tayiwu shugaban ya yanke shawara kafin ma lokacin.
A jiya Talata sakatariyar yada labaran fadar shugaban Amurka Sarah Huckabee Sanders ta ce, shugaba Trump ya yanke shawara akan Iran kuma yana so ya tabbatar da cewa Amurka ta fidda manufofi da dama da zasu tunkari batun, ba kawai wani bangarensa ba, amma a magance duk matsalolin dake tattare da Iran, a matsayin kasar da ba ta mutunta ka’idodi.
A watan da ya gabata shugaba Trump yayi subul da baka a jawabin da yayi a zauren taron majalisar dinkin duniya. Yace “Yarjejeniyar da aka kulla da Iran ita ce mafi muni, wadda ta fi amfanar bangare daya da Amurka ta taba shiga”.
Shugaba Trump ya kira wannan yarjejeniyar “abin kunya ga Amurka”. Ya kara da cewa bana tunanin kun gama jin wannan batun”.