Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Catalonia Sun Ki Janye Batun Ballewa daga Spain duk da Jinkirta Aiwatar da Shirin


'Yansandan kwantar da tarzoma suna fafatawa da 'yan rajin samun 'yancin kai a yankin Catalonia
'Yansandan kwantar da tarzoma suna fafatawa da 'yan rajin samun 'yancin kai a yankin Catalonia

Shugabannin yankin Ctalonia dake barazanar ballewa daga Spain sun raba hankalin shugabannin kasar Spain saboda sun ki janye shirin ballewa amma kuma sun jinkirta aiwatar da shirin

Shugabannin yankin Catalonia masu tsautsauran ra’ayin a ware, sun yi kememe sun ayyana yankin a matsayin mai cin gashin kansa, amma kuma sun ce ba za su fara aiwatar da shirin ballewar ta su ba, domin suna so su ba da kofar tattaunawa da gwamnatin Spain.

Yayin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin yankin na Catalonia, shugaban majalisar, Carles Puigdmont, ya yi kira ga hukumomin Madrid da su shiga tattaunawar, inda ya kara da cewa yankin ya cancanci samun ‘yancin kansa.

Wani kakakin gwamnatin Spain ta Firay Minista Mariano Rajoy, ya ce gwamnatin ta yi wancakali da ayyana ballewar da yankin daga kasar.

Kakakin ya kara da cewa, ai babu batun tattaunawa kuma, tun da shugabannin yankin na Catalonia sun riga sun ce suna son su balle.

A daren jiya Talata Puigdemont, ya kara tabbatarwa ‘yan majalisar dokokin yankin cewa, Catalonia zai bi tafarki ko kuma tsarin mulkin Jamhhuriyya ne.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG