Yayin da yake jawabi a jiya Talata a babban taron sojin kasar da ake yi na shekara-shekara, wanda ake wa lakabi da AUSA a takaice, Janar Mark Milley, ya ce kara kimtsa yanayin shirin sojin kasar, shi ne abinda fannin da yake kula da shi, zai fi maida hankali a kai.
Ya kara da cewa akwai bukatar dakarun Amurka su ci gaba da karuwa, da kuma samar da wata cibiyar horarwa ta zamani, tare da inganta fannonin fasaha, musamman a fannin rumbun adana bayanai, da kwatanta yanayi na yaki da kuma inganta fannin mutum-mutumi mai sarrafa kansa.
Ya kuma yi kira ga majalisar dokokin Amurka da ta amince da kasafin kudin da ke gabanta, domin dakarun kasar su maida hankulinsu kan bunkasa rundunonin sojin kasar.
Wadannan kalamai na Milley, na zuwa ne kwana guda bayan da sakataren tsaron Amurka, Jim Mattis ya ce dangantakar da ke tsakanin Amurka da Korea ta Arewa, za ta ta’allaka ne ta fuskar diplomisiyya, amma ya kara da cewa ya zama dole dakarun Amurka su zauna cikin shiri koda al’amura sun dagule.
Facebook Forum