Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sa Ran Shugaban Amurka Trump Zai Ki Sabunta Yarjejeniyar Shirin Nukiliyar Iran


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Ana sa ran nan da wasu kwanaki masu zuwa, Shugaban Amurka, Donald Trump, zai ayyana shirinsa na kin sabunta yarjejeniyar shirin nukiliyan Iran da aka kulla a shekarar 2015.

Shugaba Trump ya baiwa majalisar dokokin kasar kwanaki 60 su yanke shawara kan ko a sake kakaba takunkumi akan hukumomin Tehran ko kuma a’a.

Bisa tsarin doka, a ranar 15 ga watan Oktoba, shugaba Trump ya kamata yanke shawara kan wannan al’amari, amma majiyoyi a Fadarsa ta White House sun ce mai yiwuwa shawarar da zai yanke ta zo gadan-gadan.

A babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a watan da ya gabata, Trump ya nuna alamu a jawabinsa cewa matsayar da aka cimma da Iran, ita ce yarjejeniya mafi muni da Amurka ta taba kullawa.

Sai dai kin sabunta yarjejeniyar, ba zai soke matsayar da aka cimma ba, wacce Iran ta yi tsakaninta da Amurka da wasu manyan kasashen duniya, kan dakatar da shirinta na nukiliya.

Hakan kuma ba yana nufin za a maido da tsoffin takunkumin da Amurkan ta saka mata bane, amma dai kwararru da dama na ganin kin sabunta matsayar, zai haifar da maido da takunkumin da soke yarjejeniyar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG