Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Haramtawa Wasu Jiragen Ruwa Jigila Zuwa Yankin Koriya Ta Arewa


Majalisar dinkin duniya ta haramtawa wasu jiragen ruwa shiga tashoshin jiragen ruwa a duk fadin duniya saboda jigilar kayayyaki daga sassan duniya zuwa Koriya ta arewa da kuma dauko kayayyaki daga Koriya ta arewa.

Hugh Griffins, shugaban kwamitin aiwatar da takunkumin da aka kakabawa Koriya ta arewa da aka maida ita saniyar ware, shine ya bada wannan sanarwa jiya Litinin a wani taro da manema labarai.

Griffith, yace haramtawa jiragen zirga zirga ya fara aiki ne daga ranar Alhamis ta makon jiya. Kundin bayani kan jiragen ruwa ya nuna jirage da ake kira Petrel 8, da aka yiwa rijista a Comoros, da Hao Fan 6, dake amfani da tutar Saint Kitts da Nevis, da jirgin ruwan Koriya ta arewa da ake kira TONG SAN 2, jirgi na hudu shine Jie Shun, ba shi da rijista daga ko wace kasa.

A cikin watan Agusta ne kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya ya amince da wani kuduri da ya haramtawa Koriya ta arewa jigilar gawayin coal, da tama da karafa, da kuma abinci daga ruwa zuwa kasuwannin duniya, a zaman martani na nasarar gwajin makami mai linzami da zai iya ratsa nahiyoyi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG