Haka kuma akwai wasu da yawa a cikin motocin bas da ke fitowa daga wuraren shiga daban-daban tun daga juma’a, kuma har yanzu suna kan shigowa, kuma yawanci dalibai ne.
Suna kuma karban su da hannu biyo, a basu, ruwa abinci, da masauki har wani sa’I har da katin waya don su sami su kira gida. Su ka ma a bangaren su na ofishin jakadanci, dama akwai kudin da aka ware na mussaman da aka bayar saboda a tarye su da shi sannan a maryar da su Najeriya.
Ta kara da cewa, hukumomin Romania sun taimaka matuka wajen hada kai, shiri da taimako. "Ba ma gwamnati kadai ba har ma da daidaikun mutane, kungiyoyi, jami'o'i, masu zaman kansu duk sun taimaka sosai wajen ba da taimako.
Ta ce za a fara mayar da su gida idan jirgin ya isa Bucharest.
Ta kuma bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ce ta dauki nauyin jigilar 'yan Najeriyan da ke bukatar komawa.
Saurari cikakkakkiyar hirar cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5