Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabinsa na farko kan halin da kasa ke ciki a ranar Talata a gaban gamayyar majalisar dokokin Amurka, inda ya yi amfani da zafafan kalamai akan abokan gaba tare da rarrashin al’umar Amurka kan halin da suke ciki.
Amurkawa na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki baya ga annobar covid-19 ga kuma matsalar rarrabuwar kawuna da fagen siyasar kasar ke fuskanta.
Biden ya shiga zauren majalisar ne yayin da ake ta yi masa tafin nuna jinjina, shekaru biyu bayan barkewar annobar COVID-19.
A farkon jawabinsa, Biden ya ce, “a bara, annobar Covid-19 ta hana mu haduwa,” amma a karshe, ga shi mun hadu.”
An dai ga mambobin majalisar suna kada tutar kasar Ukraine a matsayin nuna goyon baya, kuma Shugaba Biden bai yi wata-wata ba, wajen yin tsokaci kan rikicin Rasha da Ukraine, inda ya bayyana cewa Amurka za ta rufe sararin samaniyarta ga dukkan jiragen saman kasar Rasha.
“Ma’aikatar shari’ar Amurka na hada wani kwamiti mai karfi, wanda zai bibiyi laifukan wasu fitattun mutane a Rasha, za mu hada kai da kawayenmu na nahiyar turai, mu rufe kadarorinsu na gidaje, jiragen ruwa da na sama, saboda haka, a wannan dare, ina mai sanar da cewa, za mu bi sahun kawayenmu wajen hana dukkan jiragen saman Rasha ratsawa ta sararin samaniyar Amurka.”
Shugaba Biden dai ya kwashe minti har goma yana magana kan batun na Ukraine inda daga baya ya tabo batutuwan da suka shafi matakan da gwamnatinsa ke dauka wajen shawo kan matsalolin da Amurkawa suke fuskanta.
Dangane da batun annobar covid-19, Biden ya ce, “saboda ci gaba da muka samu, sanadiyyar jajircewarku da matakan da muka dauka, a wannan dare, zan iya cewa, muna samun ci gaba, wajen komawa harkokinmu na yau da kullum.”
Gwamnar jihar Iowa, Kim Reynolds ce ta mayar da martani a bangaren ‘yan Repblican bayan da Shugaba Biden ya kammala jawabin nasa.