Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Na Fice Daga Ukraine-Daliba ‘Yar Najeriya


Wata daliba a Ukraine 'yar Najeriya
Wata daliba a Ukraine 'yar Najeriya

Daya daga cikin daliban da suka fice daga Ukraine zuwa makwabciya Romania ta bayyana cewa, dalibai da kansu su ka nemi hanyar ficewa daga Ukraine ba tare da taimakon hukumomi ba.

A hirar ta da Muryar Amurka, dalibar Elizabeth Iliya wadda take shekara ta hudu a jami’ar koyan aikin jinya da maganin gargajiya da kuma na zamani , da ke birnin Dnipro mai tazarar tafiyar awa takwas daga Kyiv babban birnin kasar Ukraine, ta bayyana cewa, ganin yadda ake barin wuta a manyan biranen kasar ya sa su ka nemi hanyar ficewa daga kasar ba shiri.

Yan Najeriya a Ukraine
Yan Najeriya a Ukraine

Elizabeth ta bayyana cewa, jin karar bindiga a kusa da makarantar su ya sa ita da wadansu dalibai da ke Jami’ar tsaida shawarar ficewa kafin yakin ya rutsa da su. Bisa ga cewar ta, su ne su ka nemi hanyar ficewa daga kasar tare da taimakon dillalan da ke taimakawa dalibai su iya samun saukin fara rayuwa a bakuwar kasa lokacin da su ka isa Ukraine.

Yan Najeriya a Ukraine
Yan Najeriya a Ukraine

Da aka tambaye ta ko sun fuskanci wata tsangwama lokacin da su ke kokarin shiga jirgi sai ta bayyana cewa, ita bata sami wata matsala ba, sai dai ta ji wai, an hana wadansu babaken fata shiga jirgi da farko ta kuma ga bidiyon da aka kafa a dandalin sada zumunta, amma haka bata faru a ganin idonta ba. Ta ce akwai cunkoso ainun lokacin da ta isa tashar jirgin kasan da ya zama da wahala a karbi kudin jirgi balle tantance masu shiga.

Yan Najeriya a Ukraine
Yan Najeriya a Ukraine

Dangane da batun komawa gida Najeriya, Elizabeth ta ce, akwai dalibai da suka bayyana niyar zama a kasashe da ke makwabta idan su ka sami matsuguni har zuwa lokacin da za su iya komawa Ukrain, sai dai ta bayyana niyar komawa gida da zarar ta sami takardun fita. Ta kuma bayyana irin taimakon da dalibai su ka samu daga ofishin jakadancin Najeriya a Romania da sauran kasashe da ke makwabta.

Wasu daliban Najeriya suna jiran sakamakon gwajin cutar COVID-19 yayin da suka tsallaka zuwa Hungary daga Ukraine. (AP Photo/Anna Szilagyi)
Wasu daliban Najeriya suna jiran sakamakon gwajin cutar COVID-19 yayin da suka tsallaka zuwa Hungary daga Ukraine. (AP Photo/Anna Szilagyi)

Elizabeth to bayyana cewa, ya dauke ta kwana biyu da wuni guda kafin ta isa Bucharest daga birnin Dnipro inda ta ke makaranta, kuma duk da yake sun yi tafiya da wadansu dalibai, da su ka isa Romania sun rarrabu bisa ga inda suka sami matsuguni. Bisa ga cewarta, wadansu masu aikin jinkai suka biya mata kudin otel da kuma abinci da ta isa Bucharest. Yayinda wadansu daliban suka sami matsuguni a sansanan da ofishin jakadancin Najeriya ya tanada tare da taimakon gwamnatin Romania.

Yan Najeriya a Ukraine
Yan Najeriya a Ukraine

Saurari Karin bayanin ta cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:54 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG