Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine: Najeriya Za Ta Fara Kwaso ‘Yan Kasarta , Ghana Ta Yi Jigilar Farko


'Yan Najeriya a Hungary bayan da suka tsere daga Ukraine, tare da su, jakadar Najeriya a kasar, Mrs Modupe Irele (Photo: Ofishin jakadancin Najeriya Hungary)
'Yan Najeriya a Hungary bayan da suka tsere daga Ukraine, tare da su, jakadar Najeriya a kasar, Mrs Modupe Irele (Photo: Ofishin jakadancin Najeriya Hungary)

“Tawagar farko za ta iso Najeriya a ranar Alhamis 3 ga watan Maris.” In ji ma'aikatar harkokin wajen Najeriya.

A yau iragen saman da Najeriya ta dauki shatarsu za su bar kasar don zuwa kwaso jama’arta da ke neman mafaka a wasu kasashe turai da ke makwabtaka da Ukraine mai fama da rikici.

Daruruwan ‘yan Najeriya sun tsallaka zuwa Romania, Poland, Hugary da Slovalia don tsira da ransu, bayan da Rasha ta kadammar da mamaya akan Ukraine.

Wasu daliban Ghana da aka kwaso daga Ukraine (Photo: Ma'aikatar harkokin wajen Ghana)
Wasu daliban Ghana da aka kwaso daga Ukraine (Photo: Ma'aikatar harkokin wajen Ghana)

“Muna masu ba da tabbacin cewa, wasu jiragen sama da aka yi shatarsu, za su bar Najeriya a ranar 2 ga watan Maris din 2022 don su kwaso ‘yan Najeriya.” Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar a ranar Talata ta ce.

“Tawagar farko za ta iso Najeriya a ranar Alhamis 3 ga watan Maris.” Sanarwar mai dauke da sa hannun babban Sakataren ma’aikatar Ambasada Gabriel Aduda ta kara da cewa.

A halin da ake ciki akwai ‘yan Najeriya 650 a Hungary, 350 a Poland, 940 a Romania sai 150 a Slovakia, wadanda duk ofisoshin jakadun Najeriyar ke kula da su a cewar sanarwar.

Jirgin kamfanin Max Air zai kwaso mutum 560 daga Romania, Air Peace kuma zai kwaso 364 daga Poland da wasu 360 a Hungary.

Wasu daga cikin 'yan Ghana da aka kwaso daga Ukraine (Photo: Ma'aikatar harkokin wajen Ghana)
Wasu daga cikin 'yan Ghana da aka kwaso daga Ukraine (Photo: Ma'aikatar harkokin wajen Ghana)

Rahotannin kuma daga Ghana na nuni da cewa tuni har kasar ta kwaso tawagar farko ta ‘yan kasarta da suka fice daga Ukraine.

Akasarin mutanen dalibai ne, inda hukumomin kasar suka tabbatar da kwaso mutum 17 daga cikin sama da dalibai 500 da suka makale a nahiyar ta turai.

Kididdiga ta nuna cewa, sama da mutum dubu 660 sun fice daga kasar ta Ukraine tun bayan da Rasha ta fara kai hari a ranar Alhamis.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG