Rahotanni daga karamar hukumar Suleja ta jihar Neja na nuna cewa wasu gungun matasa ne tun da farar safiya suka datsie wannan titi daidai wurin da ake kira Kaduna Road.
Sai dai jami'an tsaron sojojin Najeriya sun tarwatsa su.
"Sojoji ne suka zo suka watsar da su (kore su.)" In ji Muhammad, mazaunin yankin na Kaduna.
Shi ma Malam Sani ya ce manyan motocin Jami'an tsaro sun kai goma da suka samu nasarar korar wadannan matasa.
Sai dai Gwamnatin jihar Neja ta ce ba ta da masaniya akan wannan zanga zanga.
A wata sanarwa mai dauke da sanya hannun mai bai wa gwamnan Nejan shawara akan sha'anin labarai Aisha Wakaso, ta bukaci jama'a da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Shugaban karamar hukumar Suleja Isyaku Bawa Na'ibi ya ce Suleja wuri ne mai wuyar sha'ani shi ya sa suka dauki matakin tabbatar da zaman lafiya a garin,
Wannan na zuwa ne a daidai lokaci da hukumomin Najeriya a matakai daban daban ke ci gaba da Daukar matakan hana wannan zanga zanga da matasan kasar suka sha alwashin gudanarwa domin nuna takaici akan yadda al'ummar Najeriya ke ci gaba da shan ukubar tsadar rayuwa tun bayan cire tallafin mai da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi a bara.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5