Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zanga: ‘Yan Sanda Sun Sha Alwashin Dakile Tashe-Tashen Hankula

Sufeta Janar, Dr. Kayode Egbetokun
Sufeta Janar, Dr. Kayode Egbetokun

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a yau Juma’a tace, rundunar ta tura jami’anta dubu 4 da 200 domin shawo kan duk wani nau’in tashin hankalin da ka iya tasowa yayin zanga-zangar.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sha alwashin magance tashe-tashen hankula yayin zanga-zangar gama garin da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a yau Juma’a tace, rundunar ta tura jami’anta dubu 4 da 200 domin shawo kan duk wani nau’in tashin hankalin da ka iya tasowa yayin zanga-zangar.

Manufar tura ‘yan sandan ita ce tabbatar da tsaron al’umma da ba da kariya ga masu zanga-zangar.

Da ya ke tabbatar da hakkin mazauna birnin na gudanar da zanga-zanga, kwamishinan ‘yan sanda Abuja, Benneth Igweh, ya ba da shawarar cewa kamata ya yi a yi ta cikin lumana.

Ya ce, “kwamishinan ‘yan sanda ya sha alwashin dakile dukkanin wani nau’i na tashin hankali da rashin bin doka da oda, kasancewar ‘yan sanda ba zasu kyalle suna kallo a lalata dukiyoyin hukuma da na daidaikun mutane ko kuma a samu asarar rayuka ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG