Kiraye-kiryen na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zanga-zangar adawa da yunwa da wahalhalu a fadin kasar daga ranar 1 ga Agusta, 2024.
A cikin shawarwari ga matafiya daban-daban, kasashen uku sun gargadi 'yan kasarsu da su guji wuraren da za a iya samun arangama tsakanin hukumomin tsaro da masu zanga-zangar.
A nata shawarar, Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja ya bukaci Amurkawa da su guji gudanar da tarukan, inda ta shawarce su da su nisanta kansu daga cunkoson jama’a da zanga-zangar da kuma ci gaba da samun labarai ta kafafen yada labarai na ciki gida. https://tinyurl.com/28943fy3
Sanarwar ta kara da cewa, akwai yiwuwar toshe hanya, wuraren binciken ababen hawa, cunkoson ababen hawa, da kuma yin taho-mu-gama, inda ta bayyana cewa, “a cewar rahotannin kafafen yada labarai, ana iya samun zanga-zanga a fadin kasar a Najeriya tsakanin 29 ga Yuli zuwa 5 ga watan Agusta, 2024.
Bisa la’akari da abubuwan da suka faru a baya, zanga-zangar na iya haifar da shingaye, wuraren binciken ababen hawa, cunkoson ababen hawa, da kuma gwabzawa fada”.
Hakazalika, babbar hukumar Birtaniya ita ma ta yi gargadin cewa za a iya gudanar da zanga-zanga tsakanin ranakun 29 ga watan Yuli zuwa 10 ga watan Agusta a manyan biranen Abuja da Legas https://tinyurl.com/25j8878s.
Dandalin Mu Tattauna