Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Bari A Wargaza Kasa Ta Hanyar Zanga-Zanga Ba – Rundunar Sojin Najeriya


Manjo Janaral Edward Buba
Manjo Janaral Edward Buba

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Manjo-Janar Edward Buba ya ce duk da yake ‘yan Najeriya na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, to amma zanga-zangar da aka shata somawa a ranar 1 ga watan Agusta kan iya rikidewa zuwa tarzoma da tashin hankali, kamar yadda lamarin ya auku a kasar Kenya.

Rundunar sojin Najeriya ta yi gargadin cewa za ta dakile duk wani yunkuri na wargaza kasa, ta hanyar amfani da zanga-zangar da ‘yan kasar ke shirin farawa a wata mai fita.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Manjo-Janar Edward Buba ya fitar, ya ce duk da yake ‘yan Najeriya na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, to amma zanga-zangar da aka shata somawa a ranar 1 ga watan Agusta, kan iya rikidewa zuwa tarzoma da tashin hankali, kamar yadda lamarin ya auku a kasar Kenya.

Demonstrators carry a Kenyan flag during a protest in Nairobi, Kenya, July 23, 2024
Demonstrators carry a Kenyan flag during a protest in Nairobi, Kenya, July 23, 2024

Matasa sun bazama kan titunan birnin Nairobi suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da dokar kara harajin kayayyaki, lamarin da kuma ya rikide zuwa tashin hankali, bayan da masu zanga-zangar suka kai farmaki tare da kona wani sashe na majalisar dokokin kasar, da ma wasu kayayyakin gwamnati.

Hakan ya sa shugaban kasar ta Kenya Williams Ruto bayyana soke sabuwar dokar tare da rusa majalisar ministocinsa, to amma hakan bai kawo karshen zanga-zangar ba. An kashe mutane sama da 50 sanadiyyar zanga-zangar ta Kenya.

“Yanayin tashin hankalin da ke faruwa ba komai ba ne illa yunkuri na wargaza kasa. A kan haka ne rundunar sojin Najeriya ba za ta zura ido tana kallo ta bari kasar ta fada a cikin irin wannan yanayi ba,” in ji Janar Buba.

Ya kara da cewa “a kan wannan kuma, jami’an soji za su tsaya kai da fata, domin tabbatar da kare kasa daga irin wannan tashin hankali.”

Wannan gargadi na rundunar sojin na zuwa ne rana daya da wani gargadin da hukumar tsaron kasar na farin kaya wato DSS ta yi, inda ta ce ta gano wata makarkashiya da ake kullawa domin ta da hargitsi a kasa.

'yan Najeriya Na Zanga-Zangar Kuncin Rayuwa
'yan Najeriya Na Zanga-Zangar Kuncin Rayuwa

A cikin tata sanarwar da ta fitar, hukumar ta DSS ta ce ta gano wasu jagororin zanga-zangar da “manufarsu ita ce tumbuke gwamnati.” A kan haka DSS din ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su kauracewa shiga zanga-zangar da kuma duk wani nau’i na tashin hankali.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu wanda tuni ya soma gudanar da taruka da jami’an gwamnatinsa da jagororin al’umma, ciki har da sarakuna da malaman addini, ya bukaci ‘yan kasar da su kara hakuri, su kuma kara ba shi lokaci a yayin da gwamnatinsa ke kokarin lalubo hanyoyin magance matsalolin da ke addabar al’umma.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina:

Gargadin Rundunar Sojin Najeriya Kan Shirin Zanga-Zangar Lumana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG