Wata Kungiya A Nijar Ta Koka Da Yadda Ake Dora Alhakin Ayyukan Ta'addanci Akan Fulani

Taron Fulani makiyaya a Nijar.

A Jamhuriyar Nijar, wata kungiyar Fulani ta bayyana rashin jin dadinta dangane da yadda ake zargin Fulani da hannu a ayyukan ta’addanci da na ‘yan bindigar da suka addabi jama'ar wasu yankunan kasar saboda haka suka bukaci hukumomi su gagauta daukan matakai don kaucewa barkewar rikicin kabilanci.

Kungiyar wacce ake kira Tabital Niger a taron manema labaran da ta kira a karshen mako ta fara ne da bayyana damuwa a dangane da yanayin da aka shiga a yankunan da ake fama da hare haren ta’addanci da na ‘yan bindiga inda alamu ke nunin matsalar ta fara bijiro da wani sabon salo kamar yadda sakataren yada labaranta Alhaji Hama Oumarou ya bayyana.

Tsanantar wannan matsala akan iyakar Nijar da Mali ta tilastawa Fulanin yankin ficewa daga matsugunansu in ji Abdourahamane Alhaji Maman mazaunin karkarar Tilia.

Kungiyar na zargin wasu daga cikin ‘yan Nijar mazauna kasashen waje da yunkurin cusa irin wannan haramtacciyar akida a kawunan jama’a saboda haka ta yi kiran mahukuntan su hanzarta daukan matakai.

Kungiyar Tabital Niger ta kuma shawarci gwmantin wannan kasa ta hada gwiwa da sarakunan gargajiya don tattara shugabanin al’umomin yankunan dake fama da matsalolin tsaro akan teburi daya.

Hakan a cewarta zai sa a hada kai a tunkari aika-aikar ‘yan ta’adda da ta ‘yan bindigar dake ci gaba da haddasa barnar dukiyoyi satar dabobi har da mutuwar bayin Allah fararen hular da ba su san hawa ba su san sauka ba.

Saurari cikaken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Kungiya A Nijar Ta Koka Da Yadda Ake Dora Alhakin Ayyukan Ta'addanci Akan Fulani