Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Fulani Su Saka ‘Ya ‘Yansu a Makaranta Don Yakar Jahilci


Makiyayi a Najeriya
Makiyayi a Najeriya

Kungiyar Fuiani makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders, shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya ta gudanar da gagarumin taro a garin Lafiya, jihar Nasarawa don jan hankalin Fulani su yaki jahilci ta hanyar sanya ‘ya’yansu a makarantun addini da na zamani.

Shugaban kungiyar, reshen jahar Nasarawa, Alhaji Bala Mohammad Dabo ya ce sun tattauna ne kan hanyoyin magance matsalolin rashin zaman lafiya tsakaninsu da manoma.

Ya kara da cewa sun ja hankalin al’ummar Fulani da su sanya ‘ya’yansu a makarantu don yakar jahilci dake sanya su shiga wadansu halaye da ba su dace ba.

Yahaya Musa Jibrin dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Gindin Akwati dake karamar hukumar Barkin Ladi a jahar Filato, ya ce kungiyarsu tare da hadin gwiwan jami’an tsaro, na zakulo masu aikata laifi.

Dangantaka tsakanin makiyaya da manoma a jahar Filato ta fara armashi bayan da wani manomi mai suna Solomon a kauyen Bisichi dake karamar hukumar Barkin Ladi, ya yafe barnar da dabbobin wani makiyayi, Ibrahim suka yi masa a gonarsa.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG