Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiran Zaman Lafiyar Fulani Makiyaya Da Hausawa Da Ke Kudancin Najeriya


Fulani makiyaya
Fulani makiyaya

A yayinda ake kira ga gwamnatin Najeriya data dauki matakin hana daukan fansa da wani mai kiran kansa mai kare yancin Yarbawa Sunday Ighaho ke yi na farma Fulani, yayinda shugabannin Hausawa da Fulani na kudancin kasar su ka dukufa wajen yin kira ga makiyaya su guji daukan doka a hannunsu.

Rahotanni daga sassa daban daban na birnin Legas dai sun tabbatar da cewar babu tashin hankali a inda suke. Sai dai a yayinda ake cikin zaman wannan yanayi suma al'umman Hausawa da Fulanin da malaman addinin musulunci naci gaba da jan hankalin makiyaya da su guji shiga harkokin ta'addanci, a maimakon haka su kasance masu bin doka da oda domin zaman lafiyan Najeriya baki daya.

Wasu yan arewancin Najeriya da Muryar Amurka ta tuntunba suna cewa ya kamata su fulanin makiyaya ko su yi wa 'yan'uwansu magana ko su kalubalance su, don su daina aikata ta'addancin, kuma da su dakatar da aikin ta'asan da su ke yi.

Sun bayyana cewa sama da kashi casa'in cikin dari na masu garkuwa da mutane Fulani ne, kuma wannan ba abu ne da duk mai kaunar zaman lafiya zai lamunta ba,

Yanzu dai jama'a na jiran ganin matakan da gwamnati zata dauka na dawo da doka da oda a sassan kasar, da kuma fatar ganin an samu kwanciyan hankali da lumana a kasar.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG