NIAMEY, NIGER - Haka kuma kotun ta umarci kamfanonin da ya biyan diyya ta million 95 na cfa a matsayi na kashe laifi, to sai dai hukumar Alhazzai ta kasa ta daukaka kara domin kalubalantar wannan hukunci.
Maniyyata 158 na gungun kamfanonin Sawki Voyages ne jirgi ya bari a tasha a yayin Hajjin shekarar 2022, duk kuwa da cewa sun sami visar dake ba su izinin shiga Saudiya, lamarin da ya sa Sawki Voyages da hukumar Alhazzai wato COHO ke zargin juna da alhakin faruwarsa.
Mafari kenan aka garzaya kotu wace bayan shafe watanni kusan uku ta na sauraren bangarori ta bai wa Sawki Voyages gaskiya, kamar yadda shugaban kamfanin, Cheick Abass Ibrahim ya bayyana a taron manema labarai.
To sai dai a taron ‘yan jaridar da shugaban hukumar Alhazai ta kasa COHO Alhaji Kaigama Ibrahim ya kira, ya ce ba su gamsu da hukuncin kotun ba saboda haka tuni suka daukaka kara zuwa kotu ta gaba.
Wannan sabuwar dambarwa na wakana ne kwana guda tak bayan babban taron da ya hada masu ruwa da tsaki a tsare-tsaren ayyukan Hajji da nufin nemo bakin zaren warware tarin matsalolin da ke dabaibaye wannan haraka wace ke gudana cikin yanayin tankiya a kowace shekara a nan Nijar.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5