NIAMEY, NIGER - Ka’idodin kiwon lafiyar da hukumomin Saudiyar suka zo da su a bana sun yi nuni da cewa dole ne duk mahajjata su gabatar da takardar shaidar allurar riga kafin cutar COVID-19 da kuma wasu cututtukan da tun fil azal ba baki ba ne a sahun al’umma, kamar yadda ministan kiwon lafiyar al’umma Dr. Iliassou Idi Mainassara ya bayyana a taron manema labarai.
Akan batun cutar coronavirus, kasar Saudiya ta ce ya zama wajibi Alhazai su gabatar da takardar gwaji da ake kira Test PCR da turanci bayan takardar shaidar allurar riga kafi da ita ma ta zama dole.
Kujeru sama da 7,000 ne hukumomin Saudiya suka ware a bana domin Alhazan Jamhuriyar Nijar to amma hauhawar kudaden kujerar haji da aka fuskanta na iya zama shinge ga maniyata da dama, koda yake wasu majiyoyi na cewa an fara tattauna hanyoyin samun kudaden tallafi daga gwamnati da nufin daukar nauyin abinda ya karu akan farashin shekarun baya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: