Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Gama Jigilar Alhazanta daga Saudiya


Alhazai lokacin aikin ibada
Alhazai lokacin aikin ibada

Jagoran alhazan Nijar ya dawo da alhazan karshe inda ya bayyanawa manema labarai cewa hajjin bana ya fi sauki amma ya kira gwamnatin kasar ta soma nazarin taimakwa alhazai nan gaba

Junhuriyar Nijar ta gama jigilar alhazanta daga Saudiya zuwa gida.

jagoran alhazan, Mustapha Kadi yace duka alhazan kasar sundawo lami lafiya, har ya kara da cewa hajjin bana na da sauki ba kaman na shekarar da ta gabata ba.

Shi kuma Alhaji Sani Maikaset kira yake ga gwamnatin kasar da ta fara nazarin hanyoyin taimakawa duk masu niyar yin aikin hajji nan gaba, ta hanyar yiwa alhazanta tallafi kamar yadda wasu kasashe su ke yiwa nasu.

Alhaji Sani Maikaset yayi misali da Najeriya wadda ta ba alhazanta taimakon kudi a can Saudiya, kodayake ya amince cewa Nijar bata kai karfin arzikin Najeriya ba, amma duk da haka ta bukaci da tayi kokari.

Ga rahoton Haruna Mamman Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG