Wasu 'yan bindiga hudu suka kai hari kan wani otel da sojojin Tarayyar Turai ke anfani dashi a matsayin hekwatarsu a Bamako babban birnin kasar Mali kasar dake shan fama da hare-haren 'yan ta'ada.
Yayinda maharban suka kai hari masu gadin otel din sun fafata dasu har sun kashe daya daga cikinsu.
Bayan karawar kwamandojin sojojin Tarayyar Turai sun fitar da sanarwa a sashen sharhi na yanar gizo inda suka ce babu wani jami'insu da ya samu rauni a tashin hankalin da ya wakana kuma jami'an tsaro suna kakkabe duk wani da ka kawo la'ani a wurin.
Bayan harin babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin nan take. Wannan sabon harin na jiya ya faru ne kimanin watanni hudu da mayakan al-Qaida na yankin Islamic Maghreb suka kai kan otel din Radisson dake Bamako a Mali. A harin maharan sun kashe mutane 20 suka kuma yi kaca-kaca da otel din.
Kungiyar ce kuma ta kai hari a wurin shakatawa dake gabar teku a kasar Ivory Coast farkon wannan watan inda ta kashe mutane 19.