Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam ya kashe Sojoji da ma'aikacin Majalisar Dikin Duniya a Mali


Shugaban Kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban Kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita

Wasu da ake zargi mayakan masu tsattsauran ra’ayin Islama ne sun farmaki wani Otal din da ma’aikatan MDD ke yawan amfani da shi a kasar Mali har an hallaka sujojin Mali guda biyar da ma’aikacin MDD din guda daya.

Sannan kuma sun yi garkuwa da wasu bakin da suka sauka a Otal din. Gwamnan yankin Mopti da ke kasar Mali Kaman Kane, ya fadawa sashen faransancin Muryar Amurka cewa,

Sojojin kasar Mali sun samu kwatar mutane 4 daga cikin wadanda aka yi garkuwar dasu, amma har yanzu akwai dimbin mutanen da ake zaton ‘yan ta’addar suna rike da su a cikin Otal din mai suna Byblos.

Ba a dai bayar da jimillar bakin cikin Otal din ba, amma ance wajen yayi kaurin suna wajen karbar bakuntar ‘yan kasashen Faransa, Afirka ta Kudu, Rasha da kuma Ukraine. Sojoji dai na nan sun yiwa Otal din da’ira.

Masu tsattsauran ra’ayin addinin suna ci gaba da kai hare-hare duk da kasancewar akwai sojojin MDD na kwantar da tarzoma a kasar. Sojojin da Faransa ta jagoranta ne suka hambarar da gwamnatinsu a Arewacin Mali, bayan masu tsattsauran ra’ayin sun kwaci ikon yankin a shekarar 2012.

XS
SM
MD
LG