An ceto mutane 80 cikin wadanda 'yan ta'adda suke yin garkuwa da su daga wani hotel dake babban birnin kasar Mali, a bayan da wasu 'yan bindiga akalla 4 masu ikirarin cewa masu kishin Islama ne suka kwace hotel din, tare da kashe mutane 3 cikin mutane 170 da suka kama.
Zaratan sojoji na Mali su na bi hawa-hawa na wannan hotel mai suna Radisson Blu dake Bamako, bisa fatan kwato sauran mutanen da ake yin garkuwa da su.
Wasu rahotanni sun ce 'yan bindigar sun saki wasu daga cikin mutanen dake niya karanta ayoyin Qur'ani.
Jami'ai suka ce sojojin Majalisar Dinkin Duniya da na Mali sun kewaye hotel din. An killace dukkan hanyoyi masu zuwa hotel din. Hukumomin Mali sun roki jama'a da su zauna a gidaje ko wuraren da suke, kada su fita waje a lokacin da ake kokarin kwato hotel din.
Faransa ta tura wasu zaratan sojojinta da suka kware wajen aikin ceto mutanen da ake yin garkuwa da su.
Babu wanda ya dauki alhakin wannan lamarin, amma kasar Mali ta yi shekaru tana gwabzawa da 'yan tawaye masu alaka da kungiyar al-Qa'ida.