Mutumin nan da ake tuhuma da kokarin lalata ginin nan mai cike da tarihi na kasar Mali, yayi bayyanar farko a gaban koton kasa-da-kasa dake birnin Hogue.
A dan takaitaccen sauraren karar da aka fara ba shakka Ahmad Al Faqi ya amsa cewa sunayen sa da aka fada gaban kotu lallai haka ne shine, sai dai kuma daga nan yaki yace wani abu har aka yi aka kare zaman.
Mai gabatar da kara na kotun tace Al Mahadi ya bada umurni ko kuma shi da kansa ya taka rawa wajen rusa kaburbura da kuma masallaci a birnin Timbuktu dake kasar Mali daga watan Yuni zuwa watan Juli na shekarar 2012.
Yan tawayen nan na Islama sun karbe mulki a yawancin arewacin kasar ta Mali da farkon wannan shekarar.
Mai gabatar da karar tace Al-mahdi kuma yana daya daga cikin yan kungiyar Ansar Dine wadanda yana sahun farko na fitattun mutune da suka taka rawar ganin sun kwace ikon birnin Timbuktu.