Gwamnatin kasar Mali ta rabtaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya da wasu kungiyoyin ‘yan aware dake arewacin kasar. To sai dai ‘yan tawayen Tuareg wadanda su ne suka fi yawa sun nemi karin lokaci domin su tattauna kafin su amince.
Babbar kungiyar ‘yan awaren Tuareg da suka hada da National Movement for the Liberation of Azawad sun halarci taron sulhun da aka yi a Algiers babban Birnin kasar Algeria. Wakilan kungiyar sun ce suna bukatar a dan jirkinta yarjejeniyar na wani dan lokaci domin su cigaba da tattaunawa.
Majalisar Dinkin Duniya ce ta shirya zaman sulhun wadda manufarta ita ce kawo karshen tashin hankali a arewacin kasar.
Su dai ‘yan Tuareg suna neman nasu yankin ne inda zasu ci gashin kansu.
Tun lokacin da Tuareg suka tada kayar baya a shekarar 2012 kasar ta Mali ta shiga rikici lamarin da ya kai ga juyin mulki kana ‘yan gwagwarmayar Islama suka cafke arewacin kasar. Shigar dakarun Faransa da na kungiyar kasashen Afirka a shekarar 2013 ya taimaka aka shawo kansu.
Bangarorin biyu sun amince su tattauna a watan Yulin shekarar 2014