Bayanai daga yankin Unguwar Mai goro kusa da Alawa a karamar Hukumar shiroro na nuna cewa Yanbindigar sun Aukawa mutanen ne adai dai lokacin da suke aikin hakar Ma,adanai a wannan Wuri,
Wani da ya tsallake rijiya da baya da ya bukaci a sakaya sunanshi yace ko bayaga wadan nan mutane 8 da akaga gawarwakin wasu da dama sun fada wani wani ruwan kogi dake kusa da wannan wuri kuma har ya zuwa lokacin da muke magana dashi ba,asan yawan wadanda suka fada ruwan kiginba,
Shugaban kamar hukumar ta shiroro Hon.Akilu kuta ya tabbatar da faruwar lamarin yanda yace suna cikin yanayi na tashin hankali,
Ita ma dai Gwamnatin jihar Neja ta fitar da wata sanarwa dake nuna takaicinta akan wannan ta,addanci,
Sanarwar Mai dauke da sanya Hannun sakataren labaran Gwamna umar Bago Malam Ibrahim Bolagi tayi Allah wadai da harin dake zama na keta tare da bayyana cewa Gwamnati na kokari sosai wajan daukar matakan shawo kan matsalar rashin tsaro da ya Addabi jihar
Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar yansanda ta jihar Nejan akan wannan hari domin kuwa kokarin samun kakakin yansandan wasiu Abiodun ta wayan salula yaci tura.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5